Paparoma Francis ya yi kiran da a samar da zaman lafiya
April 16, 2017Talla
Faparoma Francis wanda ya bayyana haka a lokacin adu'oin da ya yi na bukukuwan Easter a jawabin da ya yi a dandali Saint-Pierre na Urbi da Orbi a gaban mabiya kusan dubu sitin. Ya kuma ce a kasashen Yankin Gabas ta tsakiya hade da Yemen da Siriya da Iraki akwai bukatar ci gaba da yin adu'a domin tabbatar da zaman lafiya,ya ce hakan kuwa ba zai tabbata ba, sai da hadin kan shugabanni.