1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma na son a kai kayan agaji Sudan

Ahmed Salisu
December 25, 2024

Shugaban mabiya darikar Katolika ta addinin Kirista Paparoma Francis ya bukaci da a samar da wata dama da za ta taimaka wajen shigar da kayan agaji ga wadanda yaki ya daidaita a kasar Sudan.

Papst Franziskus
Hoto: Andrew Medichini/AP/picture alliance

A jawabinsa da ya saba yi a duk ranar Kirsimeti, Paparoman ya bukaci da a yi duk mai yiwuwa wajen ganin an shigar da kayan agaji Sudan din wadda ta shafe watanni kimanin sharin tana fama da yakin basasa.

A hannu guda ya kuma bukaci da lallai a fara sabon zama da nufin ganin an cimma yarjejeniya ta zaman lafiya a kasar wadda ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye.