1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma ya fara ziyara a Afirka

James Shimanyula/Suleiman BabayoNovember 25, 2015

A wannan Laraba shugaban Kiristoci mabiya darikar katolika na duniya Paparoma Francis ya fara ziyara a kasar Kenya kafin ya zarce zuwa Yuganda da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Papst Ostern 2015 Vatikan
Hoto: Getty Images/GABRIEL BOUYS

Mahukuntan kasar Kenya sun ayyana gobe Alhamis 26.11.2015 a matsayin ranar hutu domin addu'oi na kasa domin girmama ziyarar Paparoma Francis. Abubuwa da za su gudana yayin ziyarar ta kwanaki uku, sun hada da babban taro a jami'ar birnin Nairobi gobe Alhamis, da ake sa ran mutane miliyan daya da rabi za su halarta.

Dubban Kiristoci mabiya darikar Katolika za su shiga cikin shirin na neman albarka da daga manyan limamai kimanin dubu-da-dari biyar, shirin da za a nuna kai tsaye ta tashoshin talabijin. Wadanda suka shirya bikin sun ce akwai mutane da za su halarta daga kasashe 140. Paparoma zai yi jawabi game da muhimmancin iyali, da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da nuna sanin yakamata tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Sifeto Janar na 'yan sandan kasar ta Kenya Joseph Boinett ya yi bayani kan yadda aka karfafa matakan tsaro: "A bangarenmu na 'yan sanda mun shirya masa maraba, mun shirya kabar tawagar Paparoma, da duk matakan tsaro da ake bukata a duk wuraren da zai ziyarta da bayar da tsaro ga sauran bakin da suka shiga wannan birni."

Tun farko Paparoma ya isar da sako ga 'yan Kenya da kuma bayyana dalilan ziyarar kasashen Afirka: "Ziyara ta, tana tabbatar wa mabiyar Katolika kan mahalicin da muke girmamawa da yada bushara kan muhimancin kowane ya bude zuciyarsa, musamman talakawa mabukata."

Galibin 'yan Kenya mazauna birnin Nairobi fadar gwamnatin kasar, sun nuna jin dadi da wannan ziyara ta Paparoma Francis da ke zama mafi girma tun bayan ziyarar Shugaba Barack Obama na Amirka cikin watan Yuli. "Babban rana ce mun shirya mata, babban abu ne ga mabiya Katolika." "Haka ya nuna Kenya ta bunkasa bisa addinin Kirista, kuma muna son karfafa addinin Kirista." "Haka ya zama girmamawa, mun ji dadi, babu wata dama kamar haka, haka ya yi kyau mun ji dadi muna jiransa, mun girmama wannan ziyarar zuwa Kenya." "Na ji haka a matsayin labari mai dadi saboda bai taba zuwa Afirka ba, karo na farko ke nan yake zuwa Afirka, hakan ya nuna 'yan Kenya suna nuna sha'awa da zama wani bangare na Katolika."

Kasashen gabashin Afirka suna da al'umma kimanin miliyan 194 daga ciki ake da mabiya Katolika miliyan 35. Bayan kammala ziyara a kasar Kenya, Paparoma zai wuce zuwa kasashen Yuganda, sannan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula.

Hoto: Reuters