Paparoma Francis ya gana da matasa a Filipins
January 18, 2015Talla
Bayan haka kuma Paparoman zai gana da matasa a kalla dubu 30, kafin wani zama na musamman na addu'a da zai jagoranta da yamma.
Daya daga cikin matasan mai suna Jun Chura dan shekaru 14 da haihuwa wanda wata kungiya mai fafutukar kariyar yara matasa ta Fondation ANAK-Tnk ta kubuto shi daga mugunyar rayuwar da ya samu kan shi a ciki, ya kwatanta halin rayuwar yara kanana wadanda iyayensu suka yi watsi da su ke ciki a wannan kasa, wadanda akasarin su ma suke fadawa tarkon masu lalata da kananan yara, yayin da wata yar yarinya yar shekaru 12 cikin kuka ta ke tambayar Paparoma cewa, wai don minene mutane kalilan ne ke taimakawa yara kanana.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba