Paparoma Francis ya gana da sarkin Baharain
November 3, 2022Paparoma Francis mai shekaru 85 ya isa kasar Baharain ne kan keken guragu saboda ciwon kafar da yake fama da shi. Sai dai bai hana shirya masa gagarumar tarba ta kasaita da ake wa sarakuna da shugabanin kasashe ba, saboda wannan ziyarar ita ce ta farko da ya yi a kasar ta Baharain, bayan makamanciyarta da ya kai kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a shekarar 2019.
kamar yadda Papararoma Francis ya fada wa 'yan jarida da suka tarbe shi a masaukinsa, makasudin ziyarar shi ne sada zumunci da zaburar da shugabanin addinai da siyasa na duniya da su sake zage dantse wajen tabbatar da zaman tare cikin lumana da zaman lafiya a duniya:
Paparoma ya ce: "Wannan gajeriyar ziyara ce ta kwanaki uku kacal a wannan gari mai daraja da nake kaunarsa, yake kaunata. Amma irin yayyafin ruwan da ake a yayin da na sauka filin jirgi, wata alama ce ta saukar albarka a wannan ziyarar."
Me Baharain ke jira daga Paparoma?
Mahukuntan kasar Baharain na fatan wannan ziyarar ta taka rawa wajen rage tsaurin ra'ayin addinin Islama da ta'adanci gami da nuna kyama ga Musulmi da yake kara yin kamari a kasashen Yamma da gabashin duniya.
Sheikh Abdullateef Mahmud, mukaddashin ministan kula da lamuran addini kasar ya ce: "Ta hanyar zamansa babban jakada da ke kokarin yada tausayi da kauna a duniya, muna neman shi da ya isar da irin wadannan kyawawan dabi'un ga dukannin shugabanin addinai da na siyasa wato Kiristocinsu da Musulmansu."
Paparoma da hakkin bil Adama a Baharain
Akwai kimanin Kiristoci 'yan ci rani 400,000 a kasar ta Baharain, wadanda ke zaune cikin 'yanci da walwalar addini. Sai dai kungiyar kare hakkin dan Adama ta Human Rights Watch ta nemi Paparoma da ya gaya wa mahukuntan Baharain gaskiya kan irin keta hakkin dan Adam da suke yi, musamman ga masu fafutukar neman kawo sauyin siyasa a kasar. Sannan ta yi kira a gareshi da ya matsa wa Sarkin kasar ta Baharain, Hamad bin Isa Al Khalifa da ya dakatar da zartar da hukuncin kisa da gana wa fursunoni azaba a gidajen yarin da ake zargin a nayi a kasarsa,
Paparoma Francis zai halarci wani gagarimin taron addu'a a filin wasannin kasar ta Baharain, wanda ake sa ran kimanin mutane 30,000 za su halarce shi.