Paparoma ya koka kan rikicin Al-Aqsa
July 23, 2017Talla
A jawabin da ya yi wa masu ziyarar ibada a dandalin St. Peters a wannan Lahadin, shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya yi fatan bangarorin biyu za su yi gaggawar fito da bukatar samun fahimtar juna. Arangama tsakanin Falasdinawa da jami'an 'yan sandan Isra'ila a ranar Juma'ar da ta gabata ta halaka mutane tara daga bangarorin biyu.
Masu aiko da rahotanni suka ce ana fargabar wutar rikicin ka iya karuwa. Jami'an Isra'ilan dai sun dauki tsaurara matakan tsaro ne tare da hana masallata sallah a masallacin na Al-Aqsa mai daraja ga musulmin duniya. Matakin da Isra'ilar ta gindaya shi ne sai wanda suka haura shekaru 0 da haihuwa da mata ne kadai za su sallah a masallacin maimakon kowa da kowa.