1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaVatican

Paparoma ya nemi Turai ta bude kofa ga bakin haure

Mouhamadou Awal Balarabe
September 25, 2023

Paparoma Francis ya yi kira ga kasashen Turai da su kare hakkin bakin hauren Afirika da ke jefa rayuwarsu cikin hadari a Bahar Rhum. Shugaban na darikar Katolika ta duniya ya yi bayanin a ziyararsa ta birnin Marseille.

Paparoma Francis ya yi jawabi mai susan zuciya a Marseille
Paparoma Francis ya yi jawabi mai susan zuciya a MarseilleHoto: Abaca/IMAGO

Paparoma Francis mai shekaru 86 da haihuwa ya gabatar da dogon jawabi a karshen ziyarar tasa a birnin Marseille, wacce ta samu halartar bishop 70 da matasa har ma da shugaban kasa Emmanuel Macron da mai dakinsa Brigitte. Shugaban darikar Katolika ta duniya ya yi kakkausar suka game halin ko-in-kula da kasashen Turai ke nuna wa bakin haure da ke tsallake tekun Bahar Rum da nufin inganta rayuwarsu. Sai dai wannan tsokaci ya zo a ne a daidai lokacin da aka samu kwararar bakin haure a tsibirin Lampedusa na Italiya, wanda ya haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin mambobin Kungiyar Tarayyar Turai.

Paparoma ya yi wannan maganar ne a gaban manyan jami'an Turai da dama, ciki har da ministan cikin gida na Faransa Gérald Darmanin wanda ya tabbatar da cewa kasarsa ba za ta karbi bakin hauren Lampedusa ba. Sai dai shugaban na addini ya nemi da a taimaka wa bakin hauren sajewa da al'adu na Turai maimakon tilasta musu rungumar salon rayuwa da tunani na wannan nahiya, wanda a cewarsa ke lahani ga makomarsu ta hanyar haifar da kiyayya da rashin hakuri. 

Karin bayaniPaparoma ya gana da sarkin Baharain:  

Paparoma ya gana da shugaban Faransa Emmanuel Macron a MarseilleHoto: Andreas Solaro/REUTERS

Paparoma ya tattauna da Emmanuel Macron wanda gwamnatinsa ke shirin gabatar da wata sabuwar doka kan shige da fice, lamarin da ya zafafa muhawara kan batun ba wa wasu bakin haure takardun ko izinin fara aiki. Wannan ita ce ganawa ta hudu tsakanin shugabannin biyu, wadanda ke da kyakkawar dangantaka tsakaninsu. Dama dai shugaban Katolika biliyan 1.3 na duniya ya ziyarci wata unguwa mai fama da talauci a kusa da cikin garin Marseille, inda 'yan mishan na "missionnaires de la charité" ke ba da taimako ga jama'a. A nan ma ya sake dagewa kan 'yan cude-ni-in cede-ka ba tare da la'akari da bambanci siyasa ko addini ba.


Martine Haguenin, 'yar fansho ta yaba haduwa da Paparoma inda ta ce:  "Ina ganin cewar zuwansa Marseille, hakika lokaci ne na nuna 'yan uwantaka tsakanin mabiya da wadanda ke da bambancin addini. Ina tsammanin yana da matukar muhimmanci a zauna lafiya da dukan addinai da dukanin al'adu da ke kewayen tekun Bahar Rum. Wannan wata babbar alamar hadin kai ce."    karin bayaniMutuwar Benedict na 16 ta girgiza shugabannin duniya

Bishop 70 da sauran mabiya darikar katolika sun halarci taron adu'a a MarseilleHoto: Alessandra Tarantino/AP Photo/picture alliance

Wannan ita ce ziyara ta farko da wani Paparoma ya kai Marseille na Faransa cikin kusan shekaru 500, lamarin da ya haifar da farin ciki na kusan mutane  60,000 da suka halarci taron adu'o'in da ya jagoranta. Sai dai jam'iyyun adawa na Faransa sun soki halartar taron adu'o'in da Emmanuel da Brigitte Macron suka yi, suna masu cewa ya saba wa tsarin kasar na raba masu rike da mukamai da duk wata hidima ta addini. Sai dai fadar mulki ta Elysée ta mayar da martani tana mai cewa Mista Macron bai halarci taron a matsayin Kirista ba, amma ya yi shi a matsayin shugaban kasa.