1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma zai je Iraki

Abdul-raheem Hassan
March 5, 2021

Shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis zai isa birnin Bagadaza a karon farko,a dai-dai lokacin da yankin ke fama da tashe-tashen hankula da annobar corona.

Irak Wandmalerei Papst Franziskus
Hoto: AHMAD AL-RUBAYE/AFP via Getty Images

Paparomar ya ce ziyarar tasa na zama a matsayin na musamman don yada bisharar zaman lafiya da kulla zumunci, ya kuma shirya ganawa da firaiministan Irakin Mustafa al-Kadhemi da kuma shugabannin majami'u tare da kai ziyara yankin 'yan shi'a a kudancin kasar da kuma yankun Kurdawa da ke arewacin kasar.

Rahotanni a Bagadaza na cewa an jibge dakarun tsaro a sassan kasar inda ake sa ran Paparoma zai kai ziyara, sai dai akwai wasu yankunan kasar da ke cikin dokar takaita zirga-zirga na makonni biyu don rage yaduwar cutar corona.