1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paris na goyon bayan matakan Soji a Mali

August 4, 2012

Ministan tsaron Faransa ya yi imanin cewar wannan mataki ya zamanto wajibi, na yin amfani da ƙarfin soji akan 'yan tawayen arewacin, domin ceto yankin.

A Malian family displaced by war gather at a makeshift camp in Sevare, about 600 kms (400 miles) northeast of the capital Bamako, July 11, 2012. The United States has called on Mali's authorities to accept offers by African states to send a military force to stabilise the country and help retake control of its vast northern desert, now in the hands of al Qaeda-linked Islamists. The U.N. Security Council has been reluctant to back military intervention without a clearer plan for the force. Meanwhile, regional criticism of Mali's army for a March coup has left soldiers there hesitant about the idea of foreign troops being dispatched. Picture taken July 11, 2012. REUTERS/Emmanuel Braun (MALI - Tags: POLITICS CONFLICT CIVIL UNREST TPX IMAGES OF THE DAY)
Hoto: Reuters

Ministan tsaro na Faransa Jean-Yves Le Drian, ya shaidar da cewar ƙasarsa za ta bada goyon bayanta wa yunƙurin ƙasashen Afirka na amfani da ƙarfin soji a yankin arewacin Mali da ke hannun 'yan tawaye. Sai dai duk da cewar yana da imanin hakan ya kasance wajibi, kuma akwai bukatar yinsa, Faransa ba zata kasance a sahun gaba ba. A ziyarar da ya kai birnin Lorient dake yanki arewa maso yammacin Faransa, ministan tsaron kasar ya faɗa wa manema labaru cewar, ƙasarsa bata da hurumin ƙirƙirar amfani da sojoji a Mali. Le Drian ya kara da cewar, Faransa na muradin kasashen ECOWAS da Tarayyar Afirka ta AU, su tsara shirin. Yace amfani da karfin soji a arewacin Mali ya zama wajibi, domin kasarsa a shirye take ta bada goyon bayanta, ya kuma yi fatan tarayyar turai zata bada nata goyon bayan, bisa la'akari da halin da yankin ke ciki.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman