1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

Kamaru: Sau nawa Paul Biya zai yi mulki?

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
November 6, 2025

Shugaba Paul Biya na Kamaru ya yi rantsuwar kama aiki a karo na takwas, tun bayan da ya dare kan kujerar mukin kasar a ranar shida ga watan Nuwambar 1982.

Kamaru | Zabe | Shugaban Kasa | Paul Biya | Rantsuwa | Karo na Takwas
Shugaba Paul Biya na Kamaru, yayin da ya yi rantsuwar kama aiki a karo na takwasHoto: Angel Ngwe/AP Photo/picture alliance

Shugaba Paul Biya ya yi amfani da ranar shida ga watan Nuwamba wajen harbin tsuntsaye biyu da dutse daya, na farko rantsuwar kama aiki a gaban 'yan majalisa, bayan kotun tsarin mulkin Kamaru ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben 12 ga watan Oktoban 2025. Na biyu kuwa, domin tunawa da ranar da ya hau kan kujerar mulkin kasar a wato shida ga watan Nuwambar 1982 shekaru 43 da suka gabata.

Shugaba mafi yawan shekaru a duniya

Sai dai bikin sake rantasar da Shugaba Paul Biya a matsayin shugaban kasar ta Kamaru a karo na takwas, na gudana ne a yanayi na rikicin kin amincewa da sakamakaon zabe daga madugun adawa Issa Tchiroma Bakary. Wannan lamari dai, rage armashin rantsar da shugaban mafi yawan shekaru a duniya.

Saboda hake ne Yaoundé babban birnin kasar Kamaru ya kasance karkashin tsauraran matakan tsaro, abin da ba ya rasa nasaba da kin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da madagun 'yan adawa Issa Tchiroma Bakary ya yi. Amma baya ga totocin kasar da suke kadawa a manyan titunan Kamarun, jami'an tsaro sun harba harsasai 100 da nufin taya shi murna. Sai dai shugaban kungiyar tattaunawa da sulhu Shanda Tonme ya ce: "Wannan rana ta shida ga watan Nuwamba, ba wai kawai farkon sabon wa'adi mulki ba ne ga Biya amma sabon babi ne na rabin karni ne na tarihin siyasar Kamaru."

Mulkin mutu ka raba?

A ranar shida ga Nuwamban 1982 ne  Paul Biya, da ya kasance firaministan Kamaru na wancan lokacin, ya gaji Ahmadou Ahidjo shugaban kasar Kamaru na farko bayan samun 'yancin kai. Tun daga wannan lokaci ne yake shugabantar kasar ba tare  da katsewa ba, tsawon sama da shekaru 40. Sai dai a wannan sabon zaben ba kowa ya yarda cewa ya yi nasara ba, ciki kuwa har da Tchiroma Bakary dan takarar jam'iyyar FSNC a zaben da ya gabata.

Jagoran adawar Kamaru Issa Tchiroma BakaryHoto: Desire Danga Essigue/REUTERS

A Garoua, babban birnin yankin Arewa, wasu magoya bayan shugaban 'yan adawa kamar Koyang Amos na ci gaba da nuna bacin ransu kan rashin bin doka a zaben na watan Oktobar 2025, kuma ya nemi da a amince da nasarar dan takararsu. Nasarar da Shugaba Biya ya samu a zaben shugaban kasa bayan shekaru 43 yana mulki, na ci gaba da zama abin muhawara.

Yaushe za a ga sauyi a Kamaru?

Amma duk da haka, Éric Leonel Loumou mai ba da shawara kan dabarun siyasa ya ce: "Dogon zamani da Shugaba Biya ya shafe a kan mulki wani muhimmin ginshiki ne na kwanciyar hankali ga 'yan Kamaru, duk da kalubale da kuma tsammanin samun ingantuwar tsarin rayuwa da 'yan kasa ke da shi."

A yanayi na aminci da gajiya da mulkinsa ne, rantsuwar Paul Biya a karo na takwas na tsawon wasu shekaru bakwai ta bude wani sabon mataki na mulkin mutu ka raba a lokacin da 'yan Kamaru masu karancin shekaru ke mafarkin samun shugaba da zai dace da zamaninsu.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani