1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paul Biya ya bada umarnin sakin 'yan aware

Usman Shehu Usman
August 31, 2017

A Kamaru shugaba Biya ya umarci sakin wadanda ake tsare su bisa zargin alaka da ayyukan ta'addanci sakamakon fafutaka da su ke yi domin yankin Ingilishin kasar ya samu kulawa mai kyau daga hukumomin kasar

Kamerun Präsident Paul Biya
Hoto: imago/Xinhua Afrika

Ana kallon matakin na shugaban kasar ta kamaru Paul Biya a matsayin wanni yunkurin zuba ruwa ga wutar rikincin kan yanchin masu magana da harshen turacin ingilishi a kasar da ke da yawan al'umma miliyan ashirin da biyu.

Jagorororin yankin mai magana da harshen na ingilishi da suka hada da wani lauya Felix Abor Nkongho da wani malamamin makaranta Neba Fontem Aforteka da kuma wani mai suna Paul Aya Abine, ana zarginsu ne da laifuka da su ka shafi ta'addanci da kuma tawaye wanda ke da hukunci kisa indan an same su da laifi.

An tsare yan fafutukar ne tun a watan Janairu bayan wata kungiya mai fafutukar kare hankin yankin mai magana da harshen na ingilishi ta kira wani yajin aiki, don yin kamfe wajan yanci ga  masu magana da harshen na ingilishi.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Kamaru  Issa Tchiroma Bakari ya bayyana cewar, sakin mutanen wata alama ce da ke nuni da yadda gwamnati ke bude kofofinta ga tsiraru masu magana da harshin ingilishi da ma  kungiyoyin farar hula a kasar.

''Ko da yaushe kofofin gwamanati a bude su ke, kuma za mu amince da kowane irin shiri da ke da zummar kawo karshen wannan matsalar, gwamnati a shirye ta ke ta saurari korefe-korafe da kunnan basira, kuma dole ne mu lura da cewa akwai doka da tsare, koma wace irin matsala ake fuskanta''

To sai dai jagororin fafutukar sun musanta dukkan laifukan da ake tuhumarsu akai, wanda su ka hada da cin amanar kasa, neman haddasa yakin basasa dama gudanar da kamfe na neman amfani da tsarintarayya a kasar ta Kamaru.

Kame 'yan fafutukar da gwamnatin ta yi sanadiyar rikici a yankunan masu amfani da harshen na ingilishi, abinda kuma ya haifar da durkushewar harkokin kasuwanci a yankuna. Emmanuel Forbi, wani dan kasuwa ne a Bamenda, ya kuma ce ba zai koma harkar kasuwancin ba har sai an sake dan uwansa wanda ke cikin wanda gwamnati ke tsare da su.

''Tun da sunce sun sake yan uwanmu, muna son su dawo sai mu fara sai da kayayyakin mu''

Felix Gana wanda yayan shi basu zuwa makaranta tun watan Janairu, wanda ya ce ya dau wannan matakin ne don nuna fushi da cigaba da tsare 'yan fafutukar, ya kara da cewa gwamanati ta nuna alamun cewa tana neman sulhu.

''Wannan wani muhimmin mataki ne daga gwamnati na karfafa matakan sulhu don ganin an samar da zaman lafiya a yankin da ke amfani da harshen ingilishi, a yanzu yara na za su koma makaranta, don haka wannan labari ne mai dadin ji''


Masu fashin baki dai na ganin cewa shugaba Paul Biya, ya bada kai bori ya hau ne saboda matakin da iyayen yara a yankin su ka dauka, na kin tura yara makaran a yayin da ake shirin komawa karatu a Litinin mai zuwa, bayan karewar lokacin hutu na makarantu a kasar.