Jaridun Jamus: Paul Biya ya dau hankali
October 28, 2024A sharhin da ta rubuta, jaridar die tageszeitung mai taken: Shugaban Kamaru ya kai ziyara a kasarsa. Shugaban kasa mafi tsufa a duniya na murnar dawowarsa gida bayan wani dogon lokaci, inda gidan talabijin din kasar ya dakatar da dukkan shirye-shiryensa ya fara nuna yadda jama'a ke tururuwa suna murnar dawowar Paul Biya. Al'ummar kasar sun rina kallon bikin dawowar tasa kai tsaye a akwatunan talabijin, inda jama'a suka yi jerin gwano a kan titi. Jaridar ta ce zuwansa a Kamaru dai ya kasance tamkar ziyara ce ya kai, domin shugaban mai shekaru 91 a duniya ya fi zama a kasar Switzerland fiye da kasarsa. Da wuya a bambanta tsakanin zamansa a gadon mulki da kuma zaman da yake a asibitoci masu zaman kansu.
Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta duba rikicin siyasar kasar Mozambique ne, inda ta ce an kai wa 'yan adawa hari a Mozambique an kashe wasu na hannun daman dan takarar shugaban kasa guda biyu. Kwanaki kadan gabanin sanar da sakamakon zaben shugaban kasa, rikici ya barke a Mozambique. A cewar 'yan sanda, an kai musu harin ne yayin da suka cikin mota a Maputo babban kasar. Shaidu sun ce maharan sun yi amfani da mota yayin da suka boye kansu, suka bude wuta a kan motar da 'yan siyasar da ke ciki wuta. Wannan lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da ake jiran cikakken sakamakon zabe, sai dai sakamakon wacin gadi da hukama ta fitar ya nuna jam'iyya mai mulki ta samu sama da kaso 60 cikin 100. Sakamakon da 'yan adawa suka yi ta cece-kucen cewar, yana cike da magudi.
Sai kuma jaridar Süddeutsche Zeitung, wacce ta yi sharhi kan shirin kasashen Turai na tsugunar da bakin haure a Ruwanda. Jaridar ta ci gaba da cewa, wani nau'in firgici ne da ke tattare da taron kolin EU na baya-bayan nan. Shugabannin gwamnatoci wadanda suka firgita da nasarorin jam'iyyu masu tsattsauran ra'ayi ke samu a cikin kasashe mambobin Tarayyar Turai, lamarin ya kada hankalin shugabanni. Akasarin irin wadannan jam'iyyu masu tsattsauran ra'ayi dai, suna yakin neman zabe ne da sunan kyamar baki. Don haka yanzu ala tilas wasu kasashen na EU, za su jingina batun kare hakkin dan Adam su koma daukar matakan takaita bakin haure wanda alama ta nuna masu zabe na sha'awar hakan. Babban misali shi ne wasu kasashen Tarayyar Turai kamarsu Poland da Hungary da Holland ba sa son yin amfani da dokar EU a bangaren baki.