1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Paul Biya ya yi wa sojoji garanbawul

Zakari Sadou
August 31, 2023

Shugaba Biya ya nada sabbin sojoji jim kadan bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Gabon kuma ba karon farko ba ne da hakan ke faruwa a Kamaru yayinda aka yi juyin mulki a wata kasa

Paul Biya
Hoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

Akasarin wadanda shugaban kasar ya nada 'yan kabilarsa ne inda ake kallon yin hakan na da alaka da kabilanci shi ya sa masu fashin baki kamar Yarima Ousmanou Harouna ke ganin nade naden ba mafita ba ce na kaucewa juyin mulki

Kamaru | Faretin soji a birnin YaoundeHoto: Kepseu/Xinhua/picture alliance

Paul Biya ya dare karagar mulkin Kamaru a 1982 kawo yanzu shekaru 41 yana ci gaba da mulkar Kamaru. Kuma yana ci gaba da samun goyon bayan 'yan jam'iyyarsa da ya sake tsayawa takarar zaben 2025 wanda zai bai wa shekaru 92 da haihuwa baya.

Karin bayani: 

Kamaru: Wa zai gaji Paul Biya a mulki?

Kabilanci a Kamaru ya samu gindin zama musamman ma a bangaren ma'aikatan gwamnati inda kaso 80 cikin 100 na ma'aikatan 'yan kabilar shugaban ne wannan al'amarin na ciwa 'yan Kamaru tuwo a kwarya.

Hoto: MOHAMED ABD EL GHANY/REUTERS

Yayin da nuna rashin yarda da irin jagoranci da ake yi wa jama'a ke samun goyon bayan al'umma, hakan na bai wa dakarun sojoji wata damar da za su yi amfani da ita wajen hamɓarar da gwamnati," in ji Yarima Ousmanou Harouna mai fashin baki kan al'amuran siyasa.

A kasar ta Kamaru dai babu  wanda ya aminta cewar Paul Biya shi ke shugabancin kasar saboda ana ganin iyalansa da na kusa da shi sune ke tafiyar da mulki sai abin da aka sanar da shi.

Kawo yanzu dai Paul Biya wanda shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yankin Afirka ta tsakiya CEMAC tun 2019 bai ce uffan ba kan juyin mulkin da aka yi a Gabon.