1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP na niyar watsi da karba-karba a 2023

April 6, 2022

A kokarin kauce wa mummunan rikicin cikin gida, jam'iyyar PDP mai adawa ta bude takarar shugaban kasa zuwa ga daukacin sassan tarayyar Najeriya sakamakon rabuwar ra'ayi kan inda ya kamata mulkin ya karkata.

BG zum Thema Polygamie, DW Hindi
Atiku Abubakar na da goyon bayan matansa wajen neman takara a jam'iyyar PDPHoto: Luis Tato/AFP

Har a tsakanin gwamnonin jam'iyyar PDP 13 dai ra'ayi na rabe bisa inda baki ya kamata ya karkata cikin neman mulkin tarrayar Najeriyar a zabe na gaba. A karkashin jagorancin babban attajiri kuma gwamnan Rivers Nyesom Wike dai, PDP ba ta da zabi face mayar da mulkin zuwa kudancin kasar, a yayin da shugaban gwamnonin jam'iyyar kuma gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal yake fadin cewa ko Arewa ko kafar katako. Masu neman a bude wa kowa na samun jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa kuma tsohon dan takarar jam'iyyar PDP a zabukan baya Atiku Abubakar.


Wani kwamitin da 'yan lemar suka dora wa alhakin neman mafita ya kare aikinsa tare da mika sakamako ga majalisar kolin jam'iyyar PDP domin yanke hukunci. Sai dai majiyoyi na cikin jam'iyyar sun ce kwamitin ya bada shawarar mantawa da batun karba-karbar tare da bude ta a fili a wani abun da ke zaman alamun kaucewa rikici, duk da cewar kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanadi karba-karba.

Matasa na dakon 'yan takara da za su tsire musu kitse a wutaHoto: Thomas Lohnes/epd/imago images

PDP za ta tsayar da dan takara bisa ga cancanta 

A fadar sanata Umar Tsauri da ke zaman tsohon magatakardar jam'iyyar na kasa, ya sa PDP shirin ba zata cikin jam'iyyar. Ya ce:
“ Kowane ne aka tsaida ko mai kudi ko mara su, abin da kawai ake kallo shi ne wane ne za'a tsaida ya kasance ya amshi mulki a hannu APC domin Najeriya ta sake ci gaba ko ma a maida ta yadda take da. An kai layin da wanda ya cancanci  ya tsallaka ko yana da kudi ko baya da shi. In gwamnonin nan masu kudi suka tsaida wanda suka tsaida in bai cancanta ba za'a ba su mamaki, haka kuma duk wanda yake tunanin shi wane ne, in bai cancanta ba kada kai tsammani kudi za su sa mutum ya ci zabe, A'a.”


A baya dai karfin mulki ya sa jam'iyyar ta bankara wajen kaiwa ya zuwa fitar da jagora na takarar shugaban mai tasiri. Faruk BB  Faruk na sharhi a cikin harkar jam'iyyar, kuma ya ce kokarin neman karyawar na iya tasiri ga makomar PDP a zabe na shugaban kasa.


Ya ce: “ A lokacin Jonathan saboda yana da karfin mulki a hannunsa, jam'iyya ta ba shi goyon baya duk da ba lokacin da ya kamata ya yi takara ne ba. a lokacin sun karya karba-karba saboda karfin gwamnati. To yanzu kuma suna tsoron su 'yan adawa ne, karfin dimukaradiyya na mutane su kaunace su ne kawai zai sake kai su ga gadon mulki.  To idan kuma suka bankara tsarin su ka yi kama karya za su rasa jama'a da yawa musamman na Arewa wadanda ba za su zabe su ba, kuma zai iya tasiri a kan faduwarsu zabe.”

Goodluck Jonathan ya yi sanadin rusa tsarin karba-karba a jam'iyyar PDPHoto: AP

 

Jam'iyyun APC da PDP da NNPP na shirin karawa a 2023
Koma ya take shirin kayawa a tsakanin APC da ke neman dorawa da PDP da ke da bukatar kwace goruba a hannun kuturu dai, ba banbanci kuma a fadar Sanata Rabi'u Musa na kwankwaso da ke zaman jagoran sabuwar jam'iyyar NNPP  tsakanin manyan jam'iyyun Najeriyar guda biyu game da makomar kasar.
“ APC mu muka yi ta, muna canji! canji! canji! Ashe mutanen ba su gane abin da ake nufi da canji ba. Ita kuma PDP tana ganin in ma PDP ta yi barna yanzu APC ta fita barna, saboda haka za'a yi zaben shekara ta 2023 ne tsakanin wadanda suka yi barna da wadanda suka fi barna.”

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani