1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Manyan PDP sun fara hada kai

Zainab Mohammed Abubakar
October 11, 2018

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya sanar da goyon bayansa ga dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP mai adawa, mutumin da zai kalubalanci shugaba mai ci Muhammadu Buhari a zaben shekara ta 2019.

Nigeria Bildergalerie Staatspräsidenten Olusegun Obasanjo
Hoto: Chung Sung-Jun/Getty Images

Atiku Abubakar ya kasance mataimakin tsohon shugaba Obasanjo daga shekara ta 1999-2007. Dangantaka ta yi tsami tsakanin manyan PDPn biyu, a yunkurin Obasanjo na gyara kundin tsarin mulkin Najeriya, domin bashi damar neman zarcewa a karo na uku.

Sai dai hakan ya yi karo muradun Atikun na maye gurbinsa a matsayin shugaban kasa. Kwanaki kalilan bayan lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar adawa ta PDP a birnin Fatakwal, dottaban biyu sun yi wata ganawa a mahaifar Obasanjon watau Abeokuta da ke jiharsa ta Ogun.

Inda tsohon shugaban kasar ya jaddada masa cewar, ko kadan baza'a kwatantashi da shugaba mai ci a yanzu ba, a fannin sanin makamar aiki da fannoni daban daban na mulki.