1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP ta sha kaye a kotun ƙolin Najeriya

October 31, 2011

A Najeriya kotun ƙolin ƙasar ta kori buƙatar jam'iyyar PDP na a hana ƙalubalantar nasarar zaɓen shugaba Jonathan wanda jam'iyyar CPC ta yi.

Janar Muhammadu Buhari, ɗan takaran jam'iyyar CPC a zaɓen Najeriya na banaHoto: AP

A wata alama ta kara fuskantar koma baya ga ƙoƙarin da jamiyyar PDP ke yi na kare zaben shugaban Najeriya na 2011, kotun ƙolin Najeriya ta yi watsi da karar da jamiyyar PDP ta shigar tana bukatar kotu ta yi watis da sharia'ar da jamiyyar CPC ta shigar a kotun daukaka karar Najeriyar inda take kalubalantar zaben da aka yi wa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan bisa zargin cewa an tafka magudi.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ke kada ƙuri'a lokacin zaben shugaban ƙasa a banaHoto: AP

Wannan sharia'a da kotun ƙolin Najeriya ta yanke hukunci a kanta a Abuja, ta faro ne saboda karar da jamiyyar PDP ta shigar a gaban kotun bisa cewar jam'iyyar CPC ta yi ba dai dai ba wajen shigar da kara a gaban kotu don kalubalantar zaben shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, inda ta shigar da karar a ranar Lahadi don haka jamiyyar PDP na bukatar kotun koli ta yi watsi da karar yadda jamiyyar CPC bata da wata hujja ta kalubalantar batun.

To sai dai kotun kolin Najeriyar ta ki amincewa da wannan bukata ta jamiyyar PDP na a yi wasti da wannan kara, inda ta umurci bangarorin biyu na jamiyyar CPC da PDP da su koma kotun saurararen karar zaben shugaban kasa domin jiran hukuncin da kotun daukaka kara za ta zartas a kan wannan sharia mai daukan hankali da ma za ta fayyace makomar zaben shugaban Najeriyar na bana.

Farfesa Attahiru Jega, Shugaban hukumar zaɓen Najeriya, lokacin da ya karɓi sakamakon zaɓen shugaban Najeriya na banaHoto: dapd

Barrister Ahmed Bello Muhammod ESq na cikin lauyoyin da ke kare jamiyyar CPC wanda ya yi wa manema labarai ƙarin bayani, inda yace hsari'ar ta zo dai dai da ƙa'ida.

To sai dai bangaren jamiyyar PDP sun bayyana rashin jin dadinsu da wannan hukunci, bisa dagewar cewa kwashe fiye da kwanaki 60 da aka yi ba'a saurari kararsu ba, ya faru ne saboda kotun tana hutu, kuma akwai bukatar a yi la'akari da hakkinsu a kan batu. Barrister Amaechi Nwaiwu na cikin lauyoyin da ke kare jamiyyar PDP a wannan kara, kuma shi ya bayyana hakan a madadin sauran lauyoyi da suka shigar da ƙara.

Matasa dake bore bayan ayyana sakamakon zaben NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa

Yace akwai bukatar a fassara tanaje tanajen tsarin mulkin Najeriya a matsayin doka, domin wannan tsarin mulkin ne ya bayyana yanci dukka sassa biyu da ke cikin wannan sharia, to sai dai duk da wannan kotun ƙoli ta tsaya kan cewa batun a saurari daukaka kara cikin kwanaki 60 ba wai dama bace, abu ne da ya zama wajibi.

Bisa tsari a yanzu ya zama wajibi ga kotun daukaka kara ta yanke hukunci nan da gobe Talata kafin cikar kwanaki 180 wanda shine wa'adin da tsarin mulkin Najeriyar ya tanadar na kammala wannan shari'a wacce aka fara tun daga ranar tara ga watan Mayun bana. Sakamakon sharia'ar da zai bayyana matsayin zaben shugaban Najeriyar wanda duk da bayyana shi da kasashen duniya suka yi a matsayin hallatace, ya haifar da mummunan tashin hankali da ya sanya kwamitin da ya yi bincike a kan lamarin gargadin fuksntar juyi juya hali a Najeriyar.

Mawallafiya: Pinado Abdu/ Uwais Abubakar Idris

Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani