1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Pekka Haavisto ya yi kira da a tsagaita bude wuta

April 15, 2026

Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman kan Sudan, Pekka Haavisto, ya yi kira da a tsagaita bude wuta. bayan fara yakin gwagwarmayar neman iko tsakanin Sojojin gwamnati karkashi da dakarun sa kai na RSF

Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman kan Sudan, Pekka Haavisto
Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman kan Sudan, Pekka HaavistoHoto: Odd Andersen/AFP

Fiye da fararen hula 50,000 sun mutu a fadin kasar Sudan sakamakon yakin. Sama da 'yan kasar miliyan 14 sun yi hijira; lamarin da ya haifar da daya daga cikin matsalolin jin kai da gudun hijira mafi girma a duniya.

Yanzu haka dai masu bayar da agaji na taro a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus. Berlin din ta yi alkawarin dala miliyan 24 a bana, bayan Yuro miliyan 155 da ta bayar a bara.

Ana kuma tattauna yadda za a ci gaba da samar da tallafin gaggawa tare da bullo da sabbin dabarun sake zaman sulhu tare da tallafin Masar da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.