Pilipin ta kama wani jirgin ruwa na Koriya ta Arewa
March 5, 2016Talla
Ƙasar Pilipin ta ce ta kame wani jirgin ruwan na dakon kayayakin kasuwa na Koriya ta Arewa,a kan ƙuduirin da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya zartas na ɗaukar mataki na saka takunkumi karya tattalin arziki ga Koriya ta Arewan.
Bayan gwaje-gwajen da ta yi na mayan makamai nukiliya masu cin dogon zango.Jirgin mai sunan Jin Teg mai ɗauke da kayayaki na tan dubu 6830, wanda ya taso daga Indunisiya.Yanzu haka ana tsare da shi tun kwanaki uku a gabar tekun Subic da ke a arewa maso gabashin birnin Manila.