Kotu za ta sako Oscar Pistorius,
March 31, 2023
Talla
Dokar Afirka ta Kudu ta tanadi cewa wanda aka samu da laifin kisan kai, zai iya amfana da sakin da wuri da zarar rabin hukuncin da aka yanke masa ya cikka. Dan wasan mai shekaru 36, wanda aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 13 da watanni 5 na zaman gidan yari, a shekara ta 2013 bayan kashe masoyiyarsa ya zama gwarzon dan wasa, a gudun panpalaki a gasar Olympics ta nakasasu a shekarar ta 2012.