1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magance rigingimun makiyaya da manoma

Abdullahi Maidawa Kurgwi AH/LMJ
February 15, 2022

Hadin gwiwar kungiyoyin Fulani makiyaya a Plateau da ke tarayyar Najeriya, sun yi fatali da wata sabuwar doka ta haramta kiwon dabobi a bainar jama'a da majalisar dokokin jihar ke kokarin samarwa.

Najeriya Fulani-Makiyaya
Kasashen Afirka da dama na fama rikicin manoma da makiyayaHoto: AFP/Luis Tato

Ko da yake ya zuwa yanzu dokar haramta yin kiwon dabbobin a Plateau ba ta fara aiki ba,amma majalisar dokokin  jihar ta yi wa  dokar  karatu na biyu. Tuni dai aka gabatar da kudirin dokar ga wani kwamiti da zai yi nazari a kanta kafin zama doka, kuma duk wanda ya saba ka'idojin dokar akwai tanadin hukunce-hukunce da dama ciki har da biyan tarar makudan kudi. A dangane da haka ne hadin gwiwar kungiyoyin makiyaya a Jihar ta Plateau karkashin shugabancin Nura Abdullahi suka yi fatali da kudirin dokar, sakamakon wasu dalilai.

Shi ma shugaban kwammitin sa ido game da sha'anin dokar a bangaren makiyaya, Isa Adamu Bappa ya ce sun yi nazari kan kudirorin dokar kuma sun lura idan ta fara aiki  za a kai ga cin zarafin makiyaya a Plateau kamar yadda yake faruwa yanzu haka a makwabciyarta Benue. Dangane da haka suke bai wa gwamnan jihar Simon Lalong shawarar kin rattaba hannu kan kudirin dokar. Wasu daga cikin abubuwan da dokar ta tanada sun hadar da cin tarar kudi da ba zai gaza Naira milyan daya ba, ko zaman gidan yari na shekaru biyar ga duk wanda ya karya dokar. Kazalika tilas sai makiyayan sun mallaki takardar shaida ta gwamnati kafin su iya  mallakar wurin da za su killace dabbobinsu domin kiwo.