'Yan bindiga sun saki basaraken Jos
December 31, 2021![Nigeria Boko Haram](https://static.dw.com/image/55761918_800.webp)
Talla
'Yan bindigar sun saki basaraken kauyen Gyanbos ne bayan wani artabu tsakaninsu da dakarun wanzar da zaman lafiya a jihar. Ismaila Yakubu Ajala dake zama sakataren kungiyar raya cigaba al'ummar Femawa a Najeriya ya ce har kawo yanzu babu labarin ko an biya kudin fansa ne kafin sako basaraken, kasancewar a baya wanda suka yi garkuwa da shi sun bukaci naira milyan 500.
A cikin sanarwar da babban kwamadan rundunar wanzar da zaman lafiyar ya fitar ta ce an kama kimanin mutane takwas dake da hannu a garkuwa da basaraken.