1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Poland na iya tura wa Ukraine tankokin yaki

Abdullahi Tanko Bala
January 23, 2023

Firaministan Poland Mateusz Morawiecki ya ce mai yiwuwa Warsaw ta tura wa Ukraine tankokin yaki kirar Jamus samfurin Leopard 2 ko da bata samu amincewar gwamnatin Jamus ba.

Deutschland | Kampfpanzer Leopard 2
Hoto: Peter Steffen/dpa/picture alliance

Morawiecki ya ce ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baebock ta sanar da cewar Jamus ba za ta hana Poland tura tankokin yakin ga Ukraine ba idan ta bukaci yin hakan.

Wannan dai ya sanya fata mai yawa cewa Jamus na iya bin sahun kawancen kasashe wajen baiwa Ukraine tankokin yakin.

Firaministan na Poland ya ce suna cigaba da matsin lamba akan jamus ta bada tankokin yakin yana mai cewa Jamus na da irin wadannan tankokin yaki har 350 da za a iya amfani da su da kuma wasu 200 da suke ajiye.