Shekaru 75 da balle sansanin Auschwitz
January 27, 2020Talla
Gwamnatin 'yan Nazi ta Adolph Hitler da ke mulki a Jamus a wancan lokaci ne dai, ta azabtar tare da halaka mutane sama da miliyan daya akasarinsu Yahudawa a loakcin yakin duniya na biyu.
Albarkacin wannan rana mutane sama da 200 daga cikin fursinonin da aka tsare a sansanin na Auschwitz wadanda suka tsira da rayukansu da kuma ke raye, za su halarci bikin domin bayar da shaida kan yadda rayuwa ta kasance a sansanin gwale-gwalen a wancen lokaci da nufin fadakar da duniya, a daidai lokacin da akidar kyamar Yahudawa da ma kai masu farmaki ke karuwa musamman a kasashen Turai da Amirka.
Shugabannin kasashe da na gwamnatoci kimanin 60 ake sa ran za su halarci bikin na wannan rana na birnin Auschwitz.