1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Polio ta taso a Jamhuriyar Nijar

April 29, 2020

An sake samun wasu da cutar nan da ke nakasa kananan yara a Jamhuriyar Nijar, yayin da aka koma fifita matakan dakile cutar korona da ke haddasa asarar rayuka a yanzu.

Nigeria Kinder
Hoto: Imago Images/Zuma

Hukumar Lafiya ta Duniya, ta ce an sami wasu kananan yara da aka tabbatar sun kamu da cutar shan inna wato Polio a Jamhuriyar Nijar, sakakamakon jingine aiki rigakafin cutar saboda karfin da aka bai wa COVID-19 da ake ciki a duniya a yanzu.

Hukumar lafiyar ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce polion ta kama yara biyu ne, kuma tuni ta shanye jikin daya daga cikinsu.

Ita dai cutar ta shan inna, ana samunta ne ta hanyar shan gurbataccen ruwa da ke dauke da kwayar cutar.

A farkon wannan watan ne dai Hukumar ta Lafiya da sauran masu kungiyoyin lafiya a duniya, suka sanar da dakatar da rigakafin cutar, har zuwa watan Yulin bana, abin kuma da suka ce ba mamaki ta shafi yaduwar cutar.