1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Habasha ya jinjinawa Amirka

Zulaiha Abubakar
February 18, 2020

Yayin da sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ke kammala rangadin kasashen Afirka ya tattauna batun sauye-sauye da firaministan Habasha bayan sun tabo batun rikicin kasar da Masar kan kogin Nilu.

USA Außenminister Pompeo
Hoto: picture-alliance/AP Photo/T. D. Easley

Firaminista Abiy Ahmed na Habasha ya shaidawa manema labarai cewar Amirka ta jaddada aniyar cigaba da baiwa kasar goyon baya da hadin kai a al'amuran tsaro, duk kuwa da cewar tun bayan hawan Donald Trump shugabancin kasar Amirka kasashen Afirkan ke zarginsa da yin watsi da kasashen nahiyar.

Wani masani Vladimir Antwi-Danso a jami'ar kasar Ghana ya dora alhakin mafiya yawan matsalolin da suka addabi Afirka kan kutsen tsare-tsaren Amirka a harkokin tsaron kasashen Afirka, bayan bayyana ziyarar ta sakatare Pompeo a matsayin martanin cibiyar tsaro ta Pentago kan batun rage sojoji a Afirka da kuma sabbin tsare-tsaren izinin shiga kasar da suka shafi kasashen Najeriya da Sudan da Tanzaniya da kuma Iritiriya.