1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pompeo ya ziyarci tuddan golan a Isra'ila

Abdul-raheem Hassan
November 19, 2020

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya ziyarci tuddan golan da kasar Isra'ila ta kwace daga Siriya a wani yakin kwanaki shida shekaru 53 da suka gabata.

US-Außenminister Pompeo in Israel
Hoto: Patrick Semansky/Pool/AP/picture alliance

Ziyarar Pompeo a yankunan da ke iyakar Siriya da Isra'ila, na zama irinta na farko da wani sakataren harkokin wajen Amirka ya kai a hukumance zuwa yamma da kogin Jordan.

Mr. Pompeo ya ce gwamnatin Amirka za ta ayyana yunkurin Faladsinawa na jagorantar wasu kasashen duniya na kaurace wa Isra'ila a matsayin kyamar yahudawa.

Pompeo ya yi ikirarin haramtawa duk wata kungiya da ke da alaka yunkurin kyamar yahudawa samun tallafin kudaden gwammati, sai dai bai bayyana hakikanin kungiyar da matakin zai shafa ba.