Praministan Japan Shinzo Abbe ya yi murabus
September 12, 2007Talla
Shekara ɗaya rak bayan hawan sa kan karagar mulkin ƙasar Japon ,Praministan Shinzo Abbe yayi murabus.
Shinzo Abe ya bayyana wannan sanarwa a wani taron manema labarai, da ya kira a birninTokyo.
A bayan bayan nan, Praminista Shinzo ya tsinci kansa na cikin wani hali na tsaka mai wuya , mussammman bayan zaɓen yan majalisun dokoki, inda jam´iyar sa ta sha mumuman kayi.
Tun daga wannan lokaci tarmamuwar sa ta fara dushewa a fagen siyasar ƙasar Japon.
Badaƙalar cin hanci da karɓar rashawa da a ka samu wasu ministocin sa da hannu a ciki, ta ƙara durmuwa
Wannan murabus ta hadasa wani yanayi na ruɗami a siyasar ƙasar Japon.
Bisa dukkan alamu, jam´iyar adawa wadda a halin yanzu,ke da rinjaye a majalisar dokoki, zata naɗa saban Praminsita.