Pretoria za ta kare kai a ICC kan al-Bashir
April 7, 2017Talla
A ranar Juma'an nan ce kasar Afirka ta Kudu za ta kare kanta a gaban alkalan kotun da ke hukunta masu manyan laifuka ta ICC saboda rashin kama Shugaba Omar al-Bashir na Sudan lokacin da ya kai wata ziyara a kasar.
Mahukuntan na birnin Pretoria dai na da kalubale a gabansu na kare kai bayan rashin mutunta umarnin kotun da suke gaba wajen ganin an kafata.
Masu gabatar da kara dai a kotun ta ICC na cike da fushin ci gaba da kasancewar al-Bashir bisa mulki duk da sanya sammaci na kasa da kasa a kansa a shekarar 2009 da 2010.
Ana dai tuhumarsa da laifuka 10 uku daga ciki na aikata kisan kiyashi da laifin yaki a yankin Dafur da ya yi sanadi na rayukan mutane 300,000 da sanya sama da miliyan biyu kauracewa muhallansu kamar yadda MDD ta nunar.