1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIndiya

Putin da Xi ba za su halarci taron G20 ba

Binta Aliyu Zurmi MAB
September 6, 2023

Taron G20 da birnin New-Delhi na Indiya ke daukar bakunci zai nemi cimma matsaya a kan batutuwa da dama, amma Shugaba Xi Jinping na kasar Chaina da takwaransa na Rasha Vladmir Putin ba za su halarta ba.

Vladimir Putin da Narendra Modi da Xi JinpingHoto: MIKHAIL KLIMENTYEV/AFP/Getty Images

Shugaba Xi Jinping na kasar Chaina da takwaransa na Rasha Vladmir Putin ba za su halarci taron kasashen G20 masu karfin arzikin masana'antu ba, bisa wasu dalilai. Taron da zai gudana a ranakun 9 da 10 na wannan watan na Satumba a birnin New Delhi na kasar Indiya na da nufin tattaunawa da ma cimma yarjejeniya a kan batutuwa da dama da suka jima suna kokarin lalubo mafita a kai. Sai dai ana ganin rashin halartar wadannan kasashen biyu ka iya mayar da hannu agogo baya a wannan zama da kungiyar za ta yi.

Shugaban Amirka Joe Biden ya sha alwashin yin amfani da wannan taron domin tataunawa da takwarorinsa na kawo karshen matsalar sauyin yanayi da suka jima suna musayar yawu a kai da ma batun inganta ayyukan manyan cibiyoyin bada lamuni na duniya. Shi kuwa Firaministan Japan Fumio Kishida na son amfani da wannan taron domin ganin an kawo karshen matsalar karancin abinci da ake fama da shi a duniya.