Putin na ganawa da Erdogan na Turkiyya
December 1, 2014Ranar litini (01.12.2014) , shugaba Reccep Tayyib Erdogan na kasar Turkiyya, ya karbi bakuncin takwaran sa na Rasha Vladimir Putin, a wani kokari na karfafa dangantaka tsakanin kasashen, wadanda a baya suka sha takaddama kan rikicin kasashen Syria dama na Ukraine.
Ganawar da ta kasance a Ankara babban birnin kasar Turkiyya, daga cikin batutuwan da ke kan gaba a wannan ziyara, shugabannin biyu, suna tattauna batun harkokin makamashi ganin bukatar saukin farashin gas da Turkiyya ke bukata dama kara yawan sa, gami da wasu muhimman batutuwa na diplomasiyya.
Kasar Rasha da kasashen yamma suka maida ita saniyar ware saboda rikicin Ukraine, na kokarin kyautata dangantaka ne da Turkiyyan, musamman ma ganin yadda Turkiyyar ce za ta karbi bakwancin taron koli na manyan kasashe masu karfin tattalin arziki na G20.