'Putin na Rasha ba zai hakura da manufofinsa a Ukraine ba'
July 3, 2025
Wani jami' daga fadar Kremlin ya ce shugaban Rasha Vladimir Putin ya shaida wa takwaransa na Amurka Donald Trump cewa, Rasha na son a cimma sulhu ta hanyar tattaunawa don kawo karshen yakin da ke tsakaninta da Ukraine to amma ba za ta janye daga manyan manufofinta ba.
Putin ya fada wa Trump hakan ne a wata tattaunawar wayar tarho da suka yi a ranar Alhamis inda suka magantu kan batutuwa da dama.
Rasha da Ukraine na musanyar fursunoni
A cewar mai bai wa shugaba Putin shawara kan harkokin waje, Yuri Ushakov, shugaban Amurka Trump ya sake jaddada bukatar a kawo karshen hare-haren soji cikin gaggawa a Ukraine.
Har ila yau, tattaunawar ta kuma kunshi batutuwan yankin Gabas ta Tsakiya musamman abinda ke faruwa a Gaza da kuma Iran.
Jamus za ta taimaka wa Ukraine da makaman yaki
Shugaba Putin ya jaddada cewa Rasha na ci gaba da kokarin ganin an samu maslaha ta siyasa da tattaunawa kan rikicin a cewar mista Ushakov.