Rasha n shirin yin amfani da makami mai guba
March 22, 2022Talla
Biden ya yi gargadin cewar irin wannan matakin zai haifar da martani mai tsauri daga kasashen yammacin duniya: ''Kura ta kai masa bango, abin ya fi karfinsa, ya fara yi mana kazafi cewar muna da makamai masu guba ya ce har ma da Ukraine wannan wata alama ce, cewar yana da niyar yin amfani da makamansa masu guba:'' Shugaban na Amurka ya bayyana haka ne a jajibirin taron kolin kungiyar Tarayyar Turai da zai halarta da nufin jadadda hadin kan yankin tekun Atlantika a tunkarar hare-haren Rasha, da kuma karfafa goyon baya ga Ukraine. kafin daga baya ya harlaci taron kungiyar tsaro ta NATO.