SiyasaTarayyar Rasha
Rasha: Putin na shirin sake yin takara
December 8, 2023![Rasha | Vladimir Putin | Zabe | Tazarce | Shugaban Kasa](https://static.dw.com/image/67655206_800.webp)
Talla
Kamfanin dillancin labaran Rashan na TASS ya ruwaito cewa Shugaba Vladimir Putin ya sanar da aniyarsa ta yin tazarcen, yayin da yake karrama sojojin da suka yi yaki a Ukraine da lambar girmamawa ta ake bai wa gwarazan sojojin Rashan wato "the hero of Russia gold star" a fadarsa ta Kremlin. Putin dai ya kwashe tsawon shekaru yana shugabanci a kasar Rasha kama daga matsayin firaminista da shugaban kasa na riko, sai dai ga dukkan alamu bai shirya jan birki ba.