1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin zai je Koriya ta Arewa

September 14, 2023

Koriya ta Arewa ta ruwaito Shugaba Putin na cewa ya karbi tayin da ta yi masa cikin farin ciki, ya kuma bayar da tabbacin ci gaba da karfafa zumuntar da ke tsakanin kasashen biyu.

Hoto: Mikhail Metzel/Russian President Press Office/dpa/picture alliance

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya karbi tayin kai ziyara Koriya ta Arewa a daidai lokacin da shugaban Koriyan Kim Jong Un ya kammala ziyarar da ya kai kasar Rasha. To amma ba a bayyana lokacin da ake sa ran Putin din zai ziyarci Koriya ta Arewar ba.

A ranar Laraba, Shugaba Kim na Koriya ta Arewa a yayin ganawar sa da shugaban Rasha, ya sha alwashin bai wa Shugaba Putin cikakken hadin kan da yake bukata a yakin da yake yi da kasar Ukraine.

Duk da cewa shugabannin ba su yi wa duniya bayani dala-dalla na abin da suka tattauna ba, amma masana na cewa shugaban Rasha na neman manyan makamai masu hadari da kasar Koriya ta Arewa ke da su jibge a rumbunta. Sai dai shugaban Rashan ya yi watsi da zargin da ake masa na karya ka'idar sayen makamai a wannan sabuwar alakar da ake ganin yake kullawa da Shugaba Kim Jong Un.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani