Putin ya ce Rasha za ta cimma muradanta na yakar Ukraine
December 19, 2025
Shugaba Vladimir Putin na Rasha, ya jaddada cewa Moscow za ta cimma dukkan kudurorinta da take muradi a yakinta da Ukraine karfi da yaji, idan har Kyiv ta ki amince wa da sharuddan da ta gindaya ma ta.
Mr Putin wanda ke jawabinsa na shekara ga manema labarai a fadar mulki ta Kremlin, ya nanata cewa Rasha ta kwace yankuna masu matukar muhimmanci daga hannun Ukraine, kuma kafin karewar wannan shekara, dakarun sojinta za su sake yin wani gagarumin kamu.
Wannan taron manema labarai na zuwa a daidai lokacin da aka gaza cimma sahihiyar matsaya, kan shawarwarin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na sasanta rikicin, duk kuwa da kokarin Washington na ganin an aminta da dakatar da yakin baki-daya.
Karin bayani: Kasashen EU za su bai wa Ukraine rancen euro biliyan 90
A gefe guda kuma shugaba Volodymyr Zelenskiy na Ukraine ya ce kasarsa za ta bai wa Poland shawarwari kan yadda za ta kare kanta daga hare-haren jirage marasa matuka na Rasha, tare da tabbatar da tsaro ga yankin Baltic.
Mr Zelenskiy ya bayyana hakan ne ranar, yayin taron manema labarai a Warsaw babban birnin Poland, bayan samun gayyatar shugaba Karol Nawrocki.
Karin bayani: Jamus ta shirya mika kadarorin Rasha da ke hannun wa Ukraine
Haka zalika ya mika tayi ga 'yan kasuwar Poland da su je birnin Kyiv, don a dama da su cikin aikin sake gina Ukraine, biyo bayan rancen makudan kudaden da ya samu daga Turai don fardado da Ukraine.