1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta fara kai abinci Afirka

Abdourahamane Hassane
November 17, 2023

Gwamnatin Moscow ta fara isar da hatsi da alkama kyauta zuwa wasu kasashen nahiyar Afirka a wani mataki na cika alkawari da Shugaba Vldamir Putin ya yi na taimaka wa kasahen Afirkan.

Hoto: Ameer Al Mohammedaw/dpa/picture alliance

Minista noma na Rashar Dimitri Patrouchev ya ce kasashen Somaliya da Burkina Faso na daga cikin na farko da za su cimmakar wacce tuni aka aike da ita ta jiragen ruwa wadanda za su isa a karshen wannan wata na Nuwamba. Sannan ya ce za a aika da jiragen ruwa  cike da alkamar zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da Zimbabuwe, da Mali da Eritriya wadanda za su isa kafin karshen shekara. Shugaba Vladmir Putin ya yi alkawarin tura tan dubu dari biyu na alkama zuwa ƙasashen Afirka kyauta kafin sabuwar shekara.