1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na ci gaba da toshe abinci

Abdourahamane Hassane
May 26, 2022

Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya yi gargadin cewar Rasha za ta iya taimaka wa a shawo kan matsalar kangi da duniya ta samu kai a ciki.

Russland I Russischer Präsident Putin trifft mit Regierungsmitgliedern zusammen
Hoto: Kremlin Pool/ZUMAPRESS/picture alliance

Shugaban na Rasha ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattauna batutuwa da dama da suka shafi yakin a gidan telbijan na kasar

Ya ce: ''A shirye Rasha take, ta ba da gagarumar gudunmawa wajen shawo kan matsalar abinci ta hanyar fitar da hatsi da takin zamani, muddin kasashen yamma suka janye takunkumin da suka saka mata''. Yanzu haka  dai akwai tan kusan muliyan 25 na cimmakar na kasashen duniya da ke a tashar jiragen ruwa ta Odesa da ke a kudancin Ukraine wanda Rasha ta hana a yi fiton kayyakin.