1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin ya karbi shugabanni a taron kolin BRICS

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
October 22, 2024

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya karbi bakuncin shugabannin kasashen duniya mambobin kungiyar BRICS a taron koli a Moscow da ke nuna cewa Rasha ba saniyar ware ba ce a duniya

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Hoto: Alexander Nemenov/Pool via REUTERS

Wakilai daga kasashen duniya sama da 30 ciki har da shugabnnin kasashe 24 ke halartar wannan gagarumin taro na BRICS, wadanda suka kunshi kashi 45 cikin 100 na yawan mutanen duniya, kuma kashi 35 cikin 100 na karfin tattalin arzikin duniya.

Hoto: Alexander Zemlianichenko/AP/picture alliance

Daga cikin jiga-jigan kungiyar da ke sahun gaba wajen sauka a Kazan don halartar taron, akwai shugaban China Xi Jinping da firaministan Indiya Narendra Modi da kuma shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa.

Yayin tattaunawarsu kan taron na BRICS, firaministan Indiya Narendra Modi ya yi wa shugaba Vladimir Putin tayin shiga tsakaninsu da Ukraine don sulhunta su, da nufin wanzar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.

Karin Bayani:Ana shirin bude taron kasashen BRICS a Rasha

''Ya ce hakika ka samu nasarar jagorantar gina wannan kungiya ta BRICS tsawon shekara guda da aka shafe ana fafutukar kafa ta, ina taya ka murna a kan wannan nasara da ka cimma, shekaru 15 bayan fara wannan motsi, har ma ga shi yanzu kasashen duniya na rige-rigen shiga cikinta. Kan batun rikicin Ukraine kuwa, kamar yadda na fada a baya, na yi amanna cewa kamata ya yi a warware wannan takaddama cikin ruwan sanyi, ina goyon bayan duk wani shiri na samar da zaman lafiya nan kusa. Kuma ni da kai mun samu damar tattauna wannan batu a yau''.

Karin Bayani: Taron kungiyar BRICS ya dauki hankali

Hoto: Alexander Zemlianichenko/Pool via REUTERS

Bayan kammala jawabin Mr Modi sai Putin ya fara na sa jawabin kamar haka. ''Ya ce alakar Rasha da India tana tafiya ne cikin kyakkyawan yanayi na aminci da yarda, kuma za mu ci gaba da gina ta a kan wannan gwadabe, ministocinmu na harkokin kasashen waje na ci gaba da tuntubar juna a kai a kai, batun harkokin kasuwanci da cinikayya na cikin yanayi mai kyau matuka. Kuma ina maraba da matakin India na bude babban ofishin jakadancinta a birnin Kazan, wanda zai taimaka wajen fadada dagantaka mai dadi da ke wakana a tsakaninmu yanzu haka''.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres na daga cikin mahalarta taron na BRICS, kuma zai gana da shugaba Putin, a daura da taron, don tattauna batun yakinta da Ukraine, wanda majalisar ke fatan ganin an kawo karshensa.

Karin Bayani:Masar: Kyakkyawan fata bayan shiga BRICS

Hoto: Alexander Nemenov/Pool via REUTERS

Kasashen da suka jagoranci kafa wannan kungiya sun hada da Brazil da Rasha da India da China, sai Afirka ta Kudu da Iran da Masar da Habasha da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan isarsa zauren taron, shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana Rasha a matsayin babbar aminiyar kasarsa, wadda ta taimake su tun lokacin da suke fafutukar yaki da wariyar launin fata, don haka za su ci gaba da goyon bayanta a ko da yaushe.

Taron wanda aka fara a Talatar nan, 22 ga wannan wata na Oktoba, za a kammala shi ne ranar Alhamis, 24 ga wata.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani