1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin ya kare kansa daga zargin Birtaniya

Gazali Abdou Tasawa
September 6, 2018

Fadar shugaban kasar Rasha ta Kremlin ta yi watsi da zargin da Birtaniya ta yi wa Shugaba Putin na kitsa harin gubar da aka kai wa tsohon jami'in leken asirin Rashar a birnin Salisbury.

Russland Präsident Putin Rentenreform
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Druzhinin

Fadar shugaban kasar Rasha ta Kremlin ta yi watsi da zargin da Birtaniya ta yi wa Shugaba Putin na kasancewa mutuman da ya da ba umurnin  harin guba da aka kai wa tsohon jami'in leken asirin kasar ta Rasha wato Serguei Skripal da 'yarsa Loulia a watan Maris da ya gabata a birnin Salisbury na kasar ta Birtaniya. 

A wata fira da ya yi da manema labarai a wannan Alhamis, kakakin fadar ta Kremlin Dmitri Peskov ya ce wannan zargi ba abin amincewa ba ne kuma ba za su taba amincewa da shi ba domin babu wani daga cikin mahukuntan kasar ta Rasha na koli ko na kasa da ke da hannu a cikin aikata wannan aikin assha. 

A wannan Alhamis ce dai kasar Birtaniya ta zano kai tsaye suna Shugaba Putin a matsayin wanda ya ba da umurnin kai wannan harin guba ga tsohon jami'in leken asirin kasar tasa da ke da zama a Birtaniyar. Da ma dai a wannan laraba hukumar 'yan sandar Birtaniyar ta ba da sammacin kamo wasu 'yan kasar ta Rasha su biyu da take zargi da hannu wajen kai wannan hari da guba.