1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Putin ya shawarci a tsawaita yarjejeniyar New Start

September 22, 2025

Shawarar ta Putin na zuwa ne a daidai lokacin da wa'adin yarjejeniyar da ta tanadi kawar da makaman nukiliya a tsakanin Rasha da Amurka ke kawo jiki.

Shugaban Rasha Vladimir Putin a fadar mulki ta Kremlin
Shugaban Rasha Vladimir Putin a fadar mulki ta KremlinHoto: Alexander Kazakov/ZUMA/IMAGO

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar tsawaita wa'adin yarjejeniyar kawar da makaman nukiliya da masu linzami da ke cin gajere da matsakaicin zango ta New Start da shekara guda, wadda Moscow da Washington suka kula tun a lokacin yakin cacar baka kuma ke kawo karshe a watan Fabarairu na 2026.

Mista Putin ya ce a shirye Rasha take bayan ranar biyar ga watan Fabarairu na 2026 don ci gaba da mutumta tanade-tanaden yarjejeniyar musamman ma rage yawan samar da sunadaren nukiliya, kafin daga bisani bayan nazarce-nazarce bangarorin biyu sun yanke matsaya kan dorewar yarjejeniyar.

Karin bayani: Mun fi Amurka karfin makaman nukiliya - Putin

Hakazalika shugaba Putin ya ce ya yi imanin cewa wannan mataki zai yi tasiri idan Amurka ta ba da hadin kai, sannan kuma ta kaucewa daukar matakai da za su kawo cikas ga ka'idojin da wannan yarjejeiya ta New Start ta shinfida.