1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanin Afirka sun gana da Putin

June 17, 2023

Bayan tattaunawa a Kyiv shugabannin Afirka sun kuma gana da shugaban Rasha Vladimir Putin a kokarin sasanta bangarorin biyu don kawo karshen yaki a Ukraine

Tawagar shugabbin Afirka sun gana da Putin
Hoto: AP

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yaba da matakin da ya kira adalci da kasashen Afirka suka nuna wajen kawo karshen rikicin Ukraine. Putin ya baiyana haka ne gyayin tattaunawa da tawagar Afirka da ke neman masalaha tsakanin Kiev da Moscow.

Tawagar mai karfi ta shugabannin Afirkar ta fara isa Kyiv domin gabatar da shawarwari na kawo karshen rikicin da ke yin tasiri a Afirka wajen tashin farashin hatsi.

Tawagar ta kunshi shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da na Senegal Macky Sall da shugaban Zambia Hkainde Hichilema da kuma na Comoros Azali Assoumani wanda ke shugabantar kungiyar tarayyar Afirka a yanzu.

Cyril ramaphosa ya shaida wa shugaba Putin cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen yakin ta hanyar hawa teburin tattaunawa.

Putin ya ce yana martaba matsayin kasashen Afirka na nuna goyon baya dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.