1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Putin ya yi waya da Trump kan yakin Iran

April 29, 2026

Shugabannin kasashen biyu sun tattauna yadda za a kawo karshen yakin Iran da kuma na Ukraine a ranar Laraba.

Putin ya yi waya da Trump kan yakin Iran
Putin ya yi waya da Trump kan yakin IranHoto: ZED

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Amurka, Donald Trump, kamar yadda mai ba shi shawara kan harkokin diflomasiyya, Yuri Ushakov, ya shaida wa manema labarai.

Ya ce shugabannin biyu sun fi mayar da hankali ne kan yaƙin Gabas ta Tsakiya a tattaunawa da suka shafe lokaci suna yi.

Ministan wajen Iran ya koma Pakistan kan batun sulhun Amurka

Ushakov ya bayyana cewa, shugabannin sun dubi batun halin da ake ciki dangane da Iran da kuma yankin Tekun Fasha gaba dayansa.

Ya ƙara da cewa, Putin na ganin matakin Donald Trump na tsawaita tsagaita wuta da Iran ya dace, domin hakan zai ba da damar ci gaba da tattaunawa.

Amurka da Rasha za su sake tattauna batun yakin Ukraine

Ya kara da cewa tattauna ce hanyar da za ta warware duk wata matsala tsakanin kasashen tare da kawo zaman lafiya mai dorewa.