1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha za ta kyautar hatsi ga Afirka

July 27, 2023

Shan Rasha Vladimir Putin ya yi alkawarin isar da hatsi kyauta a cikin watanni masu zuwa ga wasu kasashen Afirka guda shida.

Afrikanische Delegation zu Besuch in Russland
Hoto: Evgeny Biatov/RIA Novosti/AFP

Putin ya bayyana haka ne a jawabin bude taron da aka soma na kasashen Afirka da Rasha a Saint Petersburg da ke a arewa maso yammacin Rasha. ''A cikin watanni masu zuwa, za mu iya tabbatar da isar da hatsi tan dubu 25 zuwa dubu 50, kyauta zuwa kasashen Burkina Faso, da  Zimbabwe, da Mali, da Somaliya, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Eritrea. Taron wanda za a kammala a gobe jumaa zai kuma tattauna batun tsaro da hulda tsakanin rasha da kasashen na Afirka.