Pyongyang: Bazaranar Amirka tamkar haushin kare ne
September 21, 2017Talla
Trump dai ya yi amfani da jawabinsa na farko a babban zaman taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 da ke gudana a birnin New York na kasar ta Amirka, inda ya danganta shugaban Koriya ta Arewa a matsayin roka wanda ke kokarin saka kanshi da ma al'ummarshi wani yanayi na kunar bakin wake.
Shugaba na Amirka ya kara da cewa idan har ya zamana tilas Amirka ta kare kanta ko kuma abokan huldarta, to babu makawa illa kawai ta shafe Koriya ta Arewa daga doron kasa.
Yayin da ya isa birnin na New York wajen babban taron, ministan harkokin wajen Koriya ta Arewa Ri Yong-Ho, ya fuskanci tulin tambayoyi daga 'yan jarida, inda ya basu amsa da cewa, " masu karin magana na cewa, haushin kare ba ya hana tafiya."