Qatar 2020: An hana sayar da giya a filayen wasa
November 18, 2022Talla
Masu aiko da rahatanni suka ce Qatar din ta dauki wannan mataki a yau bayan da a baya kasar ta amince kan a sayar da barasar. To sai dai mahukuntan kasar sun ce sun kebe wasu wurare na musamman da za a sayar da bararsa amma kuma mafi akasarin wanda za su iya shiga manyan baki ne.
Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta ce ta tattauna da hukumomin Qatar inda aka amince a kebe wasu wurare da 'yan kallon za su iya sayen barasar amma fa bayan an kammala wasanni.
Qatar din dai na ci gaba da shan suka daga kasashen duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam saboda zargin da ake yi mata na tauye hakkin dan Adam.