1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Qatar ta kulla yarjejeniyar tsaro da Ukraine

March 28, 2026

Kasashen biyu sun kulla yarjejeniyar musayar kwarewa kan dabarun kariyar sararin samaniya a yayin rangadin da shugaba Zelensky na Ukraine ke yi a yakin Gabas ta Tsakiya.

Ganawar shugaban Ukraine da sarkin Qatar a birnin Doha
Ganawar shugaban Ukraine da sarkin Qatar a birnin DohaHoto: President Of Ukraine/APA Images/ZUMA/picture alliance

Qatar da Ukraine sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro a Asabar din nan, wadda ta jibanci hadin gwiwa wajen dakile barazanar makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka, kamar yadda ma'aikatar tsaron kasar da ke yankin Gulf ta bayyana a cikin wata sanarwa.

Doha da Kiev sun cimma wannan matsaya ce a yayin ziyarar da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya kai Qatar, kuma baya ga hadin gwiwa a fannonin fasaha da kuma musayar kwarewa kan dabarun kariyar sararin samaniya, kasashen biyu za su mayar da hankali kan saka hannayen jari.

A daidai wannan lokaci sojojin Iran sun ce sun kai hari kan wata ma'ajiyar na'urorin kakkabo jirage marasa matuka ta Ukraine da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, wadda a cewarsu ana amfani da ita don tallafa wa sojojin Amurka, sai dai Ukraine ta musanta wannan batu.

Saudiyya da Ukraine sun kulla yarjejeniyar tsaro

Ziyarar ta bazata da Zelensky ya kai Qatar na zuwa bayan fitowarsa daga Hadaddiyar Daular Larabawa kuma kwana guda bayan sanar da kulla wata yarjejeniyar tsaro tsakanin Ukraine da Saudiyya.