1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Rabin al'umar Sudan na fama da ja'ibar yunwa

June 27, 2024

Miliyoyin 'yan kasar Sudan ne aka yi kiyasin ke cikinmawuyin hali na bukatar abinci, sakamakon tasku da suka shiga na yaki yau sama da shekara guda ke nan.

Wasu masu dafa abincin agaji a Sudan
Wasu masu dafa abincin agaji a SudanHoto: Mohamed Khidir/Xinhua/picture alliance

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce 'yan Sudan miliyan 25 da dubu 600 ne ke ke cikin tsananin yanayi na karancin abinci, alkaluman da suka zarta rabin al'umar kasar.

Daga ciki akwai mutum dubu 755 da kecikin hali na fari sakamakon karancin ruwan sama, yayin da miliyan takwas da rabi ke cikin hali na bukatar dauki na gaggawa.

Sudan dai ta fada yaki ne cikin watan Afrilun bara, bayan barkewar rikici tsakanin bangaren gwamnati da rundunar RSF ta masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar Mohamad Hamdan Daglo.

Yakin dai ya yi sanadin salwantar rayukan dubban fararen hula, yayin kuma da miliyoyin suka tsere wa gidajensu.

Wasu dai sun makale a yankunan da ake kai hare-hare, yayin kuma da wasun ke fakewa a ketare.