1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rabon mukamai a gwamnatin kasar Jamus

Binta Aliyu Zurmi
November 26, 2021

Jam'iyyar The Greens mai rajin kare muhalli a Jamus ta san kaso kujeru da za ta samu a sabuwar gwamnatin hadaka da ake shirin kafawa a Disemba, bayan makonni na tattaunawa tsakanin jam'iyyun uku da suka kulla kwance.

Deutschland | Parteitag Bündnis90/Die Grünen
Hoto: Omer Messinger/Getty Images

The Greens ta samun ma'aikatu biyar, inda za a nada mata uku da maza biyu a sabuwar gwamnatin Jamus. 'Yar takarar shugabancin gwamnati kuma shugabar hadin gwiwa ta jam'iyyar Annalena Baerbock za ta kasance mace ta farko da za ta zama ministar harkokin wajen kasar. Shi kuwa daya shugaban jam'iyyar Robert Habeck zai zama ministan harkokin tattalin arziki da kare muhalli. Sannan an yi tayin tsohon shugaban jam'iyyar Cem Özdemir a matsayin sabon ministan noma da samar da abinci. 


A daya hannun kuwa Steffi Lemke za ta karbi ragamar kula da kare muhalli, sannan Anne Spiegel ta jihar Rhineland-Palatinate ta zama minista mai kula da harkokin iyali. Amma sai mambobin jam'iyyar The Greens sun yi zaman yanke shawarar amincewa kafin a tabbatar da nade-naden bayan rantsar da sabon shugaban gwamnatin Jamus.