1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan karfafa tattalin arziki a Jamus

Abdoulaye Mamane Amadou
March 23, 2020

Gwamnatin Jamus ta samar da wasu muhimman matakai na makudan kudade a yau Litinin domin karfafawa tsarinta na tattalin arziki a wani mataki na rage radadin annobar coronavirus ga tattalin arikin kasar.

Berlin Bundeskabinett tagt ohne Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Bensch

Sabon tsarin da majalisar ministocin kasar ta rattabawa hannu a yau din nan da ke zaman irinsa na farko tun bayan yakin duniya na biyu, zai shafi tallafin kudade ne ga ma'aikata da kamfanoni hakan da kankanan masana'antu inda gwamnatin za ta iya basu basusukan da adadin jimmalar kudin za su kai fiye da Euro biliyan "156", kamar yadda sabuwar dokar ta tanada.

A yanzu dai kallo ya koma kan majalisar dokokin kasar ta Bundestag wacce zata jefa kuri'ar na'am kan kudrin dokar a wannan makon da muke ciki.

Jamus na daya daga cikin kasashen Turai da cutar ta Covid-19 ke samun yaduwa tare da kashe mutane da dama baya ga shafuwar da take yi mata ga tattalin arziki.