1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Raguwar matsayin mutuwar yara

September 13, 2012

Hukumar da ke kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya(UNICEF) ta ce an samu ci-gaba ayakin rage matsayin mace-mace tsakanin kananan yara.

ARCHIV: Ein unterernährtes Mädchen liegt in der Klinik der Ärzte ohne Grenzen in Monrovia (Aufnahme vom 28.7.2003). Kinder trifft die Not oft besonders hart. Wenn sie schwach und hilflos sind, brauchen sie besonders viel Unterstützung. Die UN-Mitgliedsstaaten hatten im Jahr 2000 acht «Jahrtausendziele» formuliert wie die Halbierung der Zahl der Hungernden und der extrem Armen und eine deutliche Senkung der Mütter- und Kindersterblichkeit bis 2015. Tatsächlich ist der Hunger auf der Welt deutlich zurückgegangen. Das ist allerdings vor allem dem Aufschwung in Asien zu verdanken. Mit dem am Montag (20.09.2010) in New York beginnenden Armutsgipfel wollen die Vereinten Nationen bei der Bekämpfung von Hunger und Krankheit einen großen Schritt vorankommen. Foto: Nic Bothma (zu dpa 0019 - Hintergrund) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Hukumar ta ce a cikin shekaru 20 da suka gabata an samu raguwar masayin mace-macen kananan yara da kashi 50 daga cikin dari. A cikin rahoton da ta gabatar a birnin New York hukumar ta ce a shekarar da ta gabata kananan yara miliyan shida da dubu 9o0 suka mutu kafin su isa shekaru biyar. A shekarar 1990 wato shekaru 22 da suka shude kuwa adadin yaran da suka mutu ya yi miliyan 12. To amma duk da haka kusan kananan yara maza da mata dubu19 ne ke mutuwa a kowace rana daga cututtukan da za a iya magance su. Babban darekton UNICEF, Anthony Lake ya ce za a iya ceton yara da dama ta yi musu riga kafin cututtuka da sama musu abinci mai kyau da kuma magunguna. Ya ce duniya tana da fasaha da ilimi za su iya samar da wadannan abubuwa.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mouhamadou Awal Bakarabe